Gyare-gyaren Tinubu sun ƙara wa jihohi kuɗaɗe - Bala Mohammed - DCL Hausa

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin da shugaban Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun ƙara wa gwamnatocin jihohi kuɗaɗen da suke samu, tare da samar da damarmaki na bunƙasa ababen more rayuwa da inganta ayyukan gwamnati. Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hak

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce gyare-gyaren tattalin arzikin da shugaban Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa sun ƙara wa gwamnatocin jihohi kuɗaɗen da suke samu, tare da samar da damarmaki na bunƙasa ababen more rayuwa da inganta ayyukan gwamnati.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gwamna Bala Mohammed ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Bauchi, lokacin da ya karɓi bakuncin ministan kuɗi kuma mai kula da tattalin arziƙin kasa, Taiwo Oyedele, da ministan lafiya Farfesa Ali Pate, waɗanda suka kai masa ziyara.

Gwamnan ya ce gwamnatocin jihohi ba sa adawa da duk wani mataki na gwamnatin tarayya saboda kawai su yi adawa, yana mai cewa idan sun ga abin da suka yi imanin cewa yana da amfani, za su bayyana hakan.

A cewarsa, gyare-gyaren da shugaban Nijeria Tinubu ya aiwatar, musamman a fannin kuɗi da tattalin arziki, sun sa jihohi ke samun ƙarin albarkatun da za su iya amfani da su wajen gudanar da ayyukan ci gaba.

Bala Mohammed ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya kan matakan da take ɗauka a fannin kiwon lafiya, musamman gina cibiyoyin tantance cututtuka da sauran muhimman ababen more rayuwa na kiwon lafiya a sassa daban-daban na ƙasar.

Link details

Destination
dclhausa.com
Category
weblink
Language
en
Link checked
Yes
Access link →

Click the button above to access the full content of this link.

Similar pages

Share more with ShortURL

Turn long web addresses into short, easy-to-share links. ShortURL helps you share websites, resources and useful discoveries in messages, on social media and wherever your audience is.

Create a short link without an account, download its QR code, or connect your website and applications through our free API. Paste your URL and make your next link easier to share.

Create your free short link ↗