Amnesty ta yi maraba da sakin ’yar jarida Farida Isiak bisa beli - DCL Hausa

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International, ta yi maraba da sakin ’yar jarida Farida Isiak bisa beli, bayan wata kotun shari’a da ke Kawo a jihar Kaduna ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari saboda wani saƙon da ta wallafa a kafar sada zumunta kan take haƙƙin jama’a da wani sashen […]

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International, ta yi maraba da sakin ’yar jarida Farida Isiak bisa beli, bayan wata kotun shari’a da ke Kawo a jihar Kaduna ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari saboda wani saƙon da ta wallafa a kafar sada zumunta kan take haƙƙin jama’a da wani sashen ’yan sanda da ke Mararaba, Kaduna, ya yi.

Amnesty ta bayyana cewa an saki ’yar jaridar mai shekaru 23 a yammacin ranar Laraba, bayan ta shafe kwanaki a tsare.

Farida Isiak, wacce ke aiki da gidan rediyon Nagarta a Kaduna, ta samu kanta a hannun ’yan sanda ne bayan jami’an da ke ƙarƙashin jagorancin kwamandan sashen ’yan sanda na Mararaban Jos, Usman Adamu, sun kama ta da misalin ƙarfe 10 na dare ranar Litinin, 20 ga Oktoba, 2026.

Bayan kama ta, an gurfanar da ita cikin gaggawa a gaban kotun shari’a, wadda ta yanke mata hukuncin ɗaurin shekaru huɗu a gidan yari, tare da zaɓin biyan tarar naira miliyan 1.7.

Amnesty ta ce ci gaba da shirin shari’ar a ranar 3 ga Nuwamba, 2026, na nuna cewa ana hukunta ’yar jaridar ne saboda bayyana ra’ayinta da kuma fallasa zargin take haƙƙin jama’a.

Link details

Destination
dclhausa.com
Category
weblink
Language
en
Link checked
Yes
Access link →

Click the button above to access the full content of this link.

Similar pages

Share more with ShortURL

Turn long web addresses into short, easy-to-share links. ShortURL helps you share websites, resources and useful discoveries in messages, on social media and wherever your audience is.

Create a short link without an account, download its QR code, or connect your website and applications through our free API. Paste your URL and make your next link easier to share.

Create your free short link ↗