Shugabannin kananan hukumomi 21 da kansilolinsu sun fice daga PDP zuwa APC a Adamawa - DCL Hausa
Ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar APC, Ahmed Galadima, ya yi maraba da sauya shekar shugabannin ƙananan hukumomi 21 da kansiloli 226 daga jam’iyyar PDP zuwa APC, yana mai cewa matakin zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a matakai gabanin zaɓen 2027. Jaridar Punch ta ruwaito cewa Galadima ya bayyana hakan ne a ciki
Ɗan takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar APC, Ahmed Galadima, ya yi maraba da sauya shekar shugabannin ƙananan hukumomi 21 da kansiloli 226 daga jam’iyyar PDP zuwa APC, yana mai cewa matakin zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi a matakai gabanin zaɓen 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Galadima ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Adamu Sambo, ya fitar a ranar Alhamis, inda ya bayyana sauya shekar a matsayin wata muhimmiyar nasara ga APC a jihar.
Galadima ya taya shugabannin ƙananan hukumomin da kansilolin murna, yana mai cewa matakin da suka ɗauka ya nuna fahimtarsu kan sauye-sauyen da ke faruwa a siyasar Adamawa.
A cewarsa, shawarar komawarsu APC ta nuna hangen nesa a siyasa da kuma fahimtar cewa haɗin kai ga shugabanci mai manufa da jajircewa wajen bunƙasa jihar su ne ginshiƙan ci gabanta.
Ya ce sauya shekar waɗannan shugabannin siyasa na iya taimaka wa APC wajen ƙara faɗaɗa tasirinta a ƙananan hukumomi da sauran matakan siyasa na jihar.
Link details
- Destination
- dclhausa.com
- Category
- weblink
- Language
- en
- Link checked
- Yes
Click the button above to access the full content of this link.
Similar pages
Share more with ShortURL
Turn long web addresses into short, easy-to-share links. ShortURL helps you share websites, resources and useful discoveries in messages, on social media and wherever your audience is.
Create a short link without an account, download its QR code, or connect your website and applications through our free API. Paste your URL and make your next link easier to share.
Create your free short link ↗