Rikici ya ɓarke a Man United bayan shan kashi a hannun Como - DCL Hausa
Kyaftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes, da kocin ƙungiyar, Michael Carrick, sun nuna alamun saɓani kan dabarun da aka yi amfani da su a wasan da ƙungiyar ta sha kashi da ci 4-1 a hannun Como a gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League. Jaridar Punch ta ruwaito cewa rashin nasarar ta ƙara jefa makomar […]
Kyaftin ɗin Manchester United, Bruno Fernandes, da kocin ƙungiyar, Michael Carrick, sun nuna alamun saɓani kan dabarun da aka yi amfani da su a wasan da ƙungiyar ta sha kashi da ci 4-1 a hannun Como a gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa rashin nasarar ta ƙara jefa makomar Carrick cikin yanayi mara daɗi, yayin da kocin ke fuskantar suka bayan wasan da ya ba magoya bayan Manchester United da suka je kallon wasan takaici.
Bayan kammala wasan, Carrick ya nemi afuwa daga magoya bayan Manchester United kusan 700 da suka yi tafiya domin kallon ƙungiyarsu, lokacin ya tsallaka filin wasa bayan tashi daga wasan yana ɗaga hannayensa zuwa ga magoya bayan, ya ja hankalin masu kallon wasan.
Sai dai maganganun da Fernandes ya yi bayan wasan ne suka ƙara jawo hankali kan dangantakarsa da Carrick, musamman game da dabarun da ƙungiyar ta bi wajen fuskantar Como.
Da yake magana da gidan talabijin na TNT Sports a ranar Laraba bayan wasan, Fernandes ya nuna rashin gamsuwa da shawarar da ma’aikatan horarwa suka ɗauka na kin matsa wa ’yan wasan Como lamba sosai domin ƙwace musu ƙwallo.
Link details
- Destination
- dclhausa.com
- Category
- weblink
- Language
- en
- Link checked
- Yes
Click the button above to access the full content of this link.
Similar pages
Share more with ShortURL
Turn long web addresses into short, easy-to-share links. ShortURL helps you share websites, resources and useful discoveries in messages, on social media and wherever your audience is.
Create a short link without an account, download its QR code, or connect your website and applications through our free API. Paste your URL and make your next link easier to share.
Create your free short link ↗