Mun kafa sabbin rundunonin soji domin yaƙi da barazanar tsaro - Tinubu - DCL Hausa

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce rundunar sojin Nijeriya ta fara aiki da sabbin rundunonin soji a jihohin Zamfara, Kebbi, Oyo da Osun, a wani mataki da ya ce zai ƙara kusantar da jami’an tsaro da al’ummomin da ke fuskantar barazanar tsaro. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a […]

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce rundunar sojin Nijeriya ta fara aiki da sabbin rundunonin soji a jihohin Zamfara, Kebbi, Oyo da Osun, a wani mataki da ya ce zai ƙara kusantar da jami’an tsaro da al’ummomin da ke fuskantar barazanar tsaro.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana matakan da gwamnatin Nijeriya ke ɗauka domin ƙarfafa ƙarfin aiki da walwalar jami’an tsaron ƙasar.

Shugaban ya ce kafa sabbin rundunonin zai taimaka wajen kusantar da sojoji da al’ummomin da ke cikin haɗari, tare da ƙara musu damar mayar da martani cikin gaggawa idan wata barazana ta taso.

A cewarsa, sabbin rundunonin da aka fara aiki da su a Zamfara, Kebbi, Oyo da Osun wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙara ƙarfin rundunar sojin Nijeriya wajen tunkarar matsalolin tsaro.

Tinubu ya ce kasancewar sojoji kusa da al’ummomin da ke cikin haɗari zai taimaka wajen inganta saurin ɗaukar mataki idan rayukan jama’a ko dukiyoyinsu suka shiga cikin haɗari.

Link details

Destination
dclhausa.com
Category
weblink
Language
en
Link checked
Yes
Access link →

Click the button above to access the full content of this link.

Similar pages

Share more with ShortURL

Turn long web addresses into short, easy-to-share links. ShortURL helps you share websites, resources and useful discoveries in messages, on social media and wherever your audience is.

Create a short link without an account, download its QR code, or connect your website and applications through our free API. Paste your URL and make your next link easier to share.

Create your free short link ↗