Ghana ta fara neman shiga BRICS, ƙungiyar da Nijeriya ke cikinta - DCL Hausa

Gwamnatin Ghana ta amince da fara shirin neman shiga ƙungiyar ƙasashe masu tasowa ta BRICS, domin faɗaɗa dangantakarta da sauran ƙasashe da kuma ƙara samun damarmaki na bunƙasa tattalin arzikinta. TRT Afrika ta ruwaito cewa ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ne ya bayyana hakan a Accra ranar Talata

Gwamnatin Ghana ta amince da fara shirin neman shiga ƙungiyar ƙasashe masu tasowa ta BRICS, domin faɗaɗa dangantakarta da sauran ƙasashe da kuma ƙara samun damarmaki na bunƙasa tattalin arzikinta.

TRT Afrika ta ruwaito cewa ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ne ya bayyana hakan a Accra ranar Talata, bayan majalisar ministocin gwamnatin Shugaba John Dramani Mahama ta amince da matakin.

Ablakwa ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Mahama na faɗaɗa abokan hulɗar Ghana a duniya, musamman wajen jawo jarin ƙasashen waje, bunƙasa kasuwanci da samar da ƙarin damarmaki ga tattalin arzikin ƙasar.

Ministan ya ce shiga BRICS ba zai maye gurbin dangantakar Ghana da abokan hulɗartar ba ciki har da asusun ba da lamuni na duniya (IMF) da bankin duniya, sai dai zai ƙara wa ƙasar wasu zaɓuɓɓuka wajen samun haɗin gwiwa da damar ci gaba.

A cewarsa, Ghana na son samun ƙarin abokan hulɗa a fannin tattalin arziki, musamman ƙasashen da za su taimaka mata wajen samar da ayyukan yi, jawo masu zuba jari a waje da bunƙasa masana’antu.

Link details

Destination
dclhausa.com
Category
weblink
Language
en
Link checked
Yes
Access link →

Click the button above to access the full content of this link.

Similar pages

Share more with ShortURL

Turn long web addresses into short, easy-to-share links. ShortURL helps you share websites, resources and useful discoveries in messages, on social media and wherever your audience is.

Create a short link without an account, download its QR code, or connect your website and applications through our free API. Paste your URL and make your next link easier to share.

Create your free short link ↗